Yayin taron, za mu gabatar da shirye-shiryen da harsunan Sinanci, da Turanci da Rasha kai tsaye, tare da gabatar da labarai da bayanai ta harsuna 29 ta sabbin hanyoyin watsa labaru. Akwai kuma labaru ta harsuna 39 kan yanar gizo, kana za a bayar da labaru game da wannan batu ta harsuna 65 ga dukkan duniya. A hannu guda kuma, akwai hadin gwiwa tare da gidajen rediyo dake kasashen waje 130, wajen gabatar da shirye-shirye tare. (Zainab)