Kairuki ya bayyanawa wakiliyarmu a nan birnin Beijing cewa, wasu mutane sun yi tsammani burin shawarar "ziri daya da hanya daya" da Sin ta bayar shi ne fadada kasuwanni. Wannan ra'ayi kuskure ne, shawarar ta samar da damar hadin gwiwa da juna a tsakanin kasashen dake yankin Asiya, gabas ta tsakiya, Afirka har ma sauran yankuna na duniya.
Kairuki ya maida kasar Tanzania a matsayin wani misali, ya ce, bisa tsarin shawarar "ziri daya da hanya daya", kasar Tanzania za ta kara gina hanyoyin jiragen kasa, da filayen jiragen sama, da tasoshin mashigin teku da sauran ayyukan more rayuwa, ta haka za a sa kaimi ga bunkasuwar cinikayya da yawon shakatawa a Tanzania da Sin.
Hakazalika, Kairuki ya bayyana cewa, a shekarar badi za a samu hanyar jiragen sama a tsakanin kasarsa da kasar Sin kai tsaye, wanda zai kawo moriya ga sha'anin cinikayya da yawon shakatawa na kasashen biyu. Ta haka masu yawon shakatawa da 'yan kasuwa na Sin suna iya tafiya zuwa kasar Tanzania kai tsaye, kuma 'yan kasuwar kasar Tanzania suna iya zuwa kasar Sin don yin ciniki. Ta haka, bangarorin biyu za su samu moriya tare bisa tsarin shawarar "ziri daya da hanya daya". (Zainab)