Mista Li ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labaru a lokacin bikin bajen kolin Hannover Messe, wanda aka shirya a kwanan baya a kasar Jamus, inda ya kara da cewa, shirin nan na "Ziri daya da hanya daya" da gwamnatin kasar Sin ta gabatar, zai hada kan kasashen da batun ya shafa ta hanyoyin teku da na kasa. Kuma irin wannan hadin, baya ga hada kan kasashe a fannonin tattalin arziki, da cinikayya da kuma zuba jari ba, a hannu guda zai inganta ci gaban cinikayyar duk duniya baki daya, tare kuma da kawar da tasiri marasa kyau, da matsalar kudi da duniya ke fuskanta, ta yadda za a kafa wata sabuwar hanyar ci gaba. (Bilkisu)