Xi Jinping: A sa kaimi ga kasa da kasa wajen samun ci gaba tare ta hanyar "ziri daya da hanya daya"
Hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi kwas na 31 kan hanyar siliki da hanyar siliki ta teku a tarihi a ranar 29 ga watan Afrilu da yamma, inda babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS Xi Jinping ya jaddada cewa, "ziri daya da hanya daya" muhimmin mataki ne da Sin ta aiwatar a sabon yanayi, kana shi ne muhimmin dandali na samun moriyar juna. Tilas ne mu yi hangen nesa, da koyi da fasahohi daga tarihi, da yin kirkire-kirkire da gudanar da ayyuka yadda ya kamata, ta haka za a sa jama'ar kasa da kasa su san cewa za su samu moriya daga "ziri daya da hanya daya".
Mai nazari na sashen bincike kan yankunan iyakar kasa na kwalejin kimiyyar zamantakewar al'ummar kasar Sin Li Guoqiang ya yi bayani kan batun tare da bada shawara, kuma membobin hukumar siyasar sun saurari bayaninsa.
Xi Jinping ya yi jawabi a kwas din, inda ya yi nuni da cewa, hukumar siyasar ta zabi wannan batu don koyi fasahohi ta hanyar fahimtar tarihi da al'adun hanyar siliki da hanyar siliki ta teku, ta yadda za a samar da abin koyi ga aikin aiwatar da "ziri daya da hanya daya" a sabon yanayi. (Zainab)