A kwanakin baya ne dai Mr. Mubyazi ya halarci taron karawa juna sani, game da mu'amalar watsa labaru ta yanar gizo, a tsakanin kasashen dake cikin shirin "ziri daya da hanya daya", inda ya kuma bayyana wa wakilinmu na CRI cewa, kasar Tanzania ta samu gudummawa daga gwamnatin kasar Sin a fannoni da dama, kuma fannin raya yanar gizo na daya daga cikinsu.
Ya ce yanzu haka kamfanonin Sin da dama na zuba jari a Tanzania, kamar irin su kamfanin Huawei da ZTE, wadanda ke sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin sadarwa a kasar ta Tanzania. Kana Sin tana taimakawa Tanzania wajen samun ci gaba a karin wasu fannonin daban. (Zainab)