in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Kasar Sin ya yabawa dangantakar dake tsakanin kasashen Afrika da kasar Sin
2016-12-20 09:47:59 cri
Jakadan kasar Sin a Morocco Sun Shuzhong, ya ce dangantakar dake tsakanin kasashen Nahiyar Afrika da Kasar Sin na kara samun tagomashi.

Da yake jawabi yayin wani taron hadin gwiwa tsakanin kasashen nahiyar Afrika da na Asia a karon farko da ya gudana a Rabat babban birnin kasar Morocco, jakadan na kasar Sin, ya bayyana irin muhimman ci gaba da aka samu daga hadin gwiwar da Sin ta yi da kasashen Afrika, yana mai cewa, kasar Sin, za ta samar da dalar Amurka biliyan Sittin ga shirye-shiryen hadin gwiwa 10 da ta kulla da a nahiyar Afrika.

A cewarsa, Kawo yanzu, an cimma yarjeniyoyi sama da dari biyu da arba'in da jimilar kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan hamsin da miliyan dari bakwai tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.

Game da ci gaban da Morrocco ta samu kuwa, Mr Sun Shuzhong ya ce kasar ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikinta a 'yan shekarun nan, ya na mai bayyana ta a matsayin kasar da ta yi wa sauran takwarorinta fintikau wajen bunkasa tattalin arziki a nahiyar. ( Fa'iza)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China