in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Morocco ta amince da kunshin dokar tarayyar Afrika
2017-01-20 10:21:36 cri
Daukacin mambobin majalisar dokokin kasar Morocco ne suka amince da kunshin dokokin tarayya Afrika wato AU a jiya Alhamis..

Majalisar ta kuma amince da kudurin dake neman kasar ta sake shiga kungiyar AU, tare da halartar taron da za ta yi daga ranar 22 zuwa 31 na watan nan da muke ciki a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababa na Habasha.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan majalisar wakilan kasar ta amince da makamancin wannan kuduri.

Wannan mataki, ya ba gwamnatin kasar damar sake shiga kungiyar ta AU.

A ranar 10 ga watan nan ne majalisar Ministocin kasar, karkashin jagorancin Sarkin Morocco ta amince da kunshin kudurin.

A shekarar 1984 ne kasar Morocco ta fice daga kungiyar AU.

A kuma watan Satumban bara ne, kasar dake arewacin Afrika, ta bayyana bukatarta ta sake kasancewa mamba a kungiyar.

A baya-bayan nan dai, Sarkin na Morocco ya yi rangadi zuwa kasashen Afrika da dama domin neman goyon bayansu game da bukatar. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China