Cikin shekaru da dama da suka gabata, kasar Morocco ta kasance mai sai ido a kungiyar ECOWAS, inda ta halarci taruka gami da ayyuka da dama na kungiyar.
Kasar ta Morocco, wadda ke arewacin nahiyar Afirka, na da dangantaka mai karfi tsakaninta da kasashen yammacin nahiyar.
A halin yanzu, Morocco kasa ce dake kan gaba wajen zuba jari a Afirka ta yamma, sannan ita ce kasa ta biyu da ta fi zuba jari a fadin nahiyar Afirka.
A lokuta da dama cikin shekarun baya, Sarkin Morocco, ya yi tattaki zuwa kasashen Afirka ta yamma, inda ya rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama da kasashe 15 na kungiyar ECOWAS, wadanda suka taimaka sosai wajen karfafa hadin-gwiwa tsakanin Moroccon da wadannan kasashe.
A dayan bangaren kuma, Morocco ta shiga cikin harkokin wanzar da zaman lafiya a yankin Afirka ta yamma, inda ta nuna himma da kwazo wajen warware rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin.(Murtala Zhang)