in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Sin da Faransa sun zanta ta wayar tarho
2017-05-09 20:31:40 cri

A Talatar nan ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Faransa mai jiran gado Emmanuel Macron, suka zanta ta wayar tarho.

Yayin da suka tattaunawa, shugaba Xi ya taya wa Emmanuel Macron murnar zama shugaban Faransa. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin na maraba da Faransa wajen shiga aikin raya "ziri daya hanya daya". Ya ce kamata ya yi kasashen 2 su rika tuntubar juna kan al'amuran kasa da kasa da na shiyya-shiya, a kokarin ba da gudummowa wajen samun zaman lafiya, da kwanciyar hankali da wadata a duniya. Har ila yau kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan dinkuwar Turai baki daya.

A nasa bangaren, Emmanuel Macron, ya ce sabuwar gwamnatin Faransa, za ta ci gaba da bin manufar kyautata zumunci a tsakaninta da Sin, za ta kuma bi manufar "kasar Sin daya tak a duniya", tare da zurfafa hadin gwiwar kasashen 2 a fannonin jakadanci, da tattalin arziki, da ciniki, da raya masana'antu, da ma raya manufar "ziri daya hanya daya". (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China