Manzon musamman mai kula da harkokin hadin gwiwar kasashe masu tasowa na babban sakataren MDD, kuma darektan ofishin kula da hadin gwiwar kasashe maso tasowa na MDD Jorge Chediek ya bayyana cewa, kasar Sin na jagorantar hadin gwiwar kasashe masu tasowa, kuma shawarar "ziri daya hanya daya" tuni ta zama abun misali ga hadin gwiwar kasashe masu tasowa.
A yayin da yake zantawa da manema labarai, Jorge Chediek ya ce, ban da jari da fasahohi, kasar Sin tana kuma samar da dabaru da tsare-tsaren samar da ci gaban kasashen duniya, kuma dabarun kasar Sin sun cancanta a yi koyi da su.(Lubabatu)