Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a Talatar nan a birnin Beijing cewa, gamuwa da wahala ko kalubale yayin da ake aiwatar da shawarar "ziri daya hanya daya", ba wani abu ne da ya shallake hankali ba, kuma za a kai ga warware su yadda ya kamata.
Kalaman na Mr. Geng na zuwa ne a gabar da wasu ke rade radin cewa, ba za a iya aiwatar da kudurorin dake cikin shawarar nan ta "ziri daya hanya daya" yadda ya kamata ba,
A karshen wannan mako ne dai, za a gudanar da taron dandalin tattaunawar koli, game da hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya, dangane da shawarar "ziri daya hanya daya" a nan birnin Beijing.
A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa, Geng Shuang ya ce, manufar gudanar da taron na wannan karo shi ne, takaita kyawawan fasahohi, da tsara shiri, da nazari kan matsaloli, a kokarin tinkarar kalubale cikin hadin gwiwa. (Tasallah Yuan)