Da ya ke karin haske game da tattaunawar, shugaban hukumar siyasa da harkokin da suka shafi doka na kwamitin tsakiya na JKS Meng Jianzhu, ya ce nauyi ne da ya rataya a wuyan dukkan kasashe su karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin tsaro, ta yadda za a magance duk wata barazanar tsaro da shirin Ziri daya da hanya daya ke fuskanta.
Meng ya kuma yi kira ga mahalarta taron, da su yi cikakken amfani da abubuwan da aka tattauna a taron ta hanyar musayar muhimman bayanai da inganta hadin gwiwar tsaro da kuma dokoki.
Jami'in ya ce, shirin ya kara samar da ci gaban hadin gwiwa a fannonin cinikayya da zuba jari da samar da muhimman kayayyakin more rayuwa, yana mai cewa, dandalin hadin gwiwa game da shirin na Ziri daya da hanya daya dake tafe, zai kara bunkasa hadin gwiwa a ragowar fannonin rayuwa
Bayanai na nuna cewa, ya zuwa yanzu dai sama da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 100 ne suka shiga shirin na Ziri daya da hanya daya, shirin da kasar Sin ta gabatar da nufin hade yankin Asiya da Turai da kuma nahiyar Afirka ta harkokin cinikayya da muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a. (Ibrahim)