Mita Kamau ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, a yayin da yake ganawa da manema labaru a birnin New York, yana mai cewa, an gabatar da shirin "Ziri daya da hanya daya" bisa tushen neman cimma moriyar juna, da samun nasara tare. Karkashin wannan shiri kuma, ana iya ganin cewa, hakika kasashe dababn daban suna cikin wata duniyar ta karfafa hadin kai, da tabbatar da samun ci gaba tare, a maimakon ci da gumin juna.
Ban da wannan kuma, mista Kamau ya nuna cewa, abubuwan dake cikin shirin "Ziri daya da hanya daya" da suka shafi raya muhimman ababen more rayuwar jama'a, na jawo hankulan kasashen Afirka, ciki har da Kenya. A ganin sa, idan kasar Kenya da kasashen dake makwabtaka da ita, su iya kyautata wasu ayyuka a fannonin hanyar mota, da fannin zirga-zirgar jiragen sama, da jigilar kayayyaki ta teku, da fannin sadarwar yanar gizo ta intanet da dai sauransu, nan gaba kuma suka yi cudanya da kasashe daban daban na duniya karkashin shirin "Ziri daya da hanya daya", hakan zai inganta bunkasuwar tattalin arzikinsu yadda ya kamata. (Bilkisu)