in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda masu kiyaye zaman lafiya na Sin da na Nijeriya sun yi atisayen soja na hadin gwiwa
2017-05-08 10:42:10 cri
A ranar 6 ga wata a kasar Liberia, runduna ta rukuni na biyar ta 'yan sanda masu kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin dake kasar Liberia da 'yan sanda masu kiyaye zaman lafiya na Nijeriya sun yi atisayen soja na hadin gwiwa mai taken "karfin kiyaye zaman lafiya na shekarar 2017 na Sin da Nijeriya".

Tawagar musamman ta MDD dake kasar Liberia ta karbi bakuncin yin atisayen sojan, bisa jagorancin rundunar 'yan sanda masu kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin, an gudanar da shirin da ya mai da hankali kan yadda za a tinkari rikice-rikice a bakin aiki.

An ce, an yi atisayen sojan don inganta karfin hadin gwiwa wajen gudanar da aikin tare a tsakanin rundunar 'yan sandan Sin da ta kasar Nijeriya da tawagar MDD dake kasar Liberia don shirya tinkarar sabuwar barazana da kalubale da watakila za a fuskanta a nan gaba a yankunan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China