in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin cinikin dake tsakanin Sin da Nijeriya ya kai dallar Amurka biliyan 1.69 cikin watanni biyu da suka gabata
2017-03-26 13:37:42 cri
Bisa kididdigar da hukumar kwastan ta kasar Sin ta yi, an ce, a watan Janairu da watan Fabrairu na shekarar bana, adadin ciniki dake tsakanin kasar Sin da Nijeriya ya kai dalar Amurka biliyan 1.69, adadin da ya karu da kashi 10.2 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a shekarar da ta wuce. Ciki har da adadin hajojin da kasar Sin ta fitar zuwa Nijeriyar wanda ya kai darajar dalar Amurka biliyan 1.42, wanda ya karu da kashi 4 bisa dari, yayin da shigar da hajoji daga Nijeriya mai darajar dalar Amurka miliyan 270, adadin da ya karu da kashi 61.1 bisa dari.

Bugu da kari, an ce, a watan Fabrairu, Nijeriya ta ci gaba da kasance matsayi na uku cikin jerin manyan abokan cinikin kasar Sin a nahiyar Afirka, yayin da kasar Afirka ta Kudu tana kan matsayin farko, sa'an nan, kasar Angola tana matsayi na biyu cikin jerin kasashen.

Bugu da kari, adadin cinikin dake tsakanin Sin da Nijeriya ya kai kashi 6.9 bisa dari cikin adadin cinikin dake tsakanin kasar Sin da dukkan kasashen nahiyar Afirka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China