in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Nijeriya, an yi maraba ga masu zuba jari na kasar Sin
2017-03-04 13:14:15 cri

Gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo dake kudu maso yammacin Nijeriya, ya ce gwamnatinsa ta yi maraba da masu zuba jari na kamfanonin Kasar Sin.

Abiola Ajimobi ya bayyana haka ne jiya a Ibadan babban birnin jihar, yayin da yake karbar bakuncin tawagar masu zuba jari na kasar Sin, karkashin jagorancin Lin Jing, jami'i a ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya.

Gwamnan ya shaidawa bakin nasa cewa, gwamnatinsa ta kulla dangantaka da wasu 'yan kasuwar kasar Sin da dama, a wani bangare na sabon tsarinta na tabbatar da ciniki cikin 'yanci a kan hanyar Ibadan zuwa Lagos.

Gwanan ya kara da cewa, yana sa ran aiki da karin wasu kamfanonin kasar Sin a fannonin noma, makamashin hasken rana da kayayyakin more rayuwa.

Ya ce ya dauki mataki karfafa hulda da kasar Sin ne la'akari da gagarumin ci gaba da tattalin arzikinta ya samu.

A nasa bangare, Lin Jing ya ce manufar ziyarar ita ce, kara karfafa dangantaka tsakanin gwamnatin kasar Sin da ta jihar Oyo. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China