in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mata 'yan kunar bakin wake uku sun mutu sanadiyyar wani hari da suka yi niyyar kai wa, wanda bai yi nasara ba
2017-05-05 09:58:28 cri
Rundunar 'yan sandan jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya, ta ce wasu mata uku 'yan kunar bakin wake uku sun mutu, bayan bam da suke dauke da shi ya tashi, lokacin da jami'an tsaro suka dakile yunkurinsu na kai hari kan wani sansanin sojin jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan Murtala Ibrahim ya bayyana cewa, an tunkari 'yan kunar bakin waken, wadanda suka yi jigida da ababen fashewa a kofar shiga bataliya ta 195 na rundunar sojin Nijeriya dake birnin Maiduguri.

Murtala Ibrahim ya ce, 'yan kunar bakin waken sun tada bam din dake jikinsu, al'amarin da ya yi sanadin mutuwarsu tare da raunata wani soja guda.

Ya kuma shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua tuni harkokin suka koma daidai a wajen da al'amarin ya auku, bayan jami'an sashen kwance bam na rundunar sun tabbatar da babu sauran barazana.

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasar NEMA, ta ce 'yan kunar bakin waken 'yan mata ne matasa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China