Mai magana da yawun hukumar tsaro ta DSS Tony Opuiyo , ya fada cikin wata sanarwar da ta iske kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Legas birnin kasuwanci na kasar cewar, an kama hamshakin dan kasuwar tare da wasu 'yan siyasa a ranar Jumma'ar da ta gabata, saboda zarginsa da laifin sace man fetur wanda hukumar man fetur ta kasar (NNPC) ta ajiye a gidan mansa a birnin Ikko.
An kiyasta kudin man ya kai naira biliyan 11 kwatankwacin dala miliyan 34.
Opuiyo ya kara da cewa, matakin da Ubah ya dauka tamkar yin zagon kasa ne ga tattalin arzikin kasar, kuma matakin zai iya yin illa ga ci gaban tattalin arzikin Najeriyar, kana lamarin barazace ga zaman lafiyar kasar kuma ya saba dokar gwamnati. (Ahmad Fagam)