Majiyar ta shedawa Xinhua cewa, an sako 'yan matan ne biyowa bayan wata yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin Najeriyar da mayakan masu tsattsauran ra'ayi.
Sakin 'yan matan ya zo ne wata guda bayan da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa tana kokarin yin hadin gwiwa da hukumomin kasashen waje masu shiga tsakani domin ganin an sako 'yan matan na sakandaren Chibok.
Shugaban na Najeriya ya fada a ranar 14 ga watan Aprilun a cikin wata sanarwar da ya gabatar yayin da 'yan matan ke cika shekaru 3 da yin garkuwa da su inda ya bayyana cewa, a shirye gwamnatinsa take ta tabbatar an sako 'yan matan na Chibok.
Shugaba Buhari ya ce, gwamnati na ci gaba da tuntubar masu shiga tsakani da kuma hukumomin tsaro na sirri na cikin gida domin tabbatar da sakin raguwar 'yan matan da sauran mutanen da mayakan na Boko Haram ke yin garkuwa da su.
Kana ya shedawa iyayen yaran da sauran 'yan Najeriya cewa, kada su fidda tsammanin dawowar raguwar 'yan matan na sakandaren Chibok da ake garkuwa da su. (Ahmad Fagam)