in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban bankin Najeriya ya dakatar da wasu bankuna 14 daga sayar da kudaden kasashen waje
2017-05-04 09:14:54 cri
Babban bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da wasu bankunan ajiya 14 na kasar daga shirin sayarwa kanana da matsakaitan masana'antan kasar kudaden kasashen waje da gwamnatin kasar ta bullo da shi a kwanaki baya.

Kakakin babban bankin Najeriyar Isaac Okorafor ya bayyana cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a birnin Legas cibiyar kasuwancin kasar cewa, an dakatar da bankunan ne biyo bayan korafe-korafen da jama'a ke yi cewa, wasu daga bankunan na gurgunta wannan tsari da ganganta ta hanyar hana kananan da matsakaitan masana'antun cin gajiyar wannan tsari da babban bankin kasar ya tanadar.

A saboda haka, babban bankin na CBN ya yanke shawarar dakatar da bankunan da suka karya doka bayan ya yi la'akari da rahotannin da ya samu wadanda suke nuna cewa, tun lokacin da aka kaddamar da wannan shiri zuwa wannan lokaci, bankuna 22 ne kadai suka sayarwa kanana da matsakaitan masana'antun kasar kudaden ketare.

Okorafor ya ce CBN bai ji dadin matakin da bankunan suka dauka ba na kin sayarwa kanana da matsakaitan masana'antun kasar kudaden ketaren, ta yadda za su samu damar shigo da kayayyakin da suke bukata duk da wannan tsari da babban bankin ya tanadar musu.

Yanzu haka dai babban bankin Najeriyar ya gargadi dukkan bankunan da suka ki sayarwa kananan da matsakaitan masana'antun kasar kudaden ketare bayan da suka kammala raba sama da dala miliyan 300 ta hanyar wannan tsari tun lokacin da aka kaddamar da shi a watan da ya gabata, babu makawa za su fuskanci takunkumi kamar yadda doka ta tanada. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China