in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya na kiyaye shawarwarin likitoci
2017-05-04 09:49:25 cri
Ministan labarai da al'adu na Nijeriya Lai Muhammad, ya ce shugaban kasar Muhammadu Buhari na bin shawarwarin likitocinsa domin ya samu sauki baki daya.

Ministan ya bayyana haka ne ga manema labarai a jiya, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa na mako-mako, inda ya ce Shugaba Buhari zai ci gaba da hutawa ba tare da yin wasu ayyuka ba kamar yadda likitocinsa suka bada shawara.

Mataimakin Shugaban kasar, Yemi Osinbajo ne ya jagoranci taron da ya gudana a fadar shugaban kasa dake Abuja babban birnin kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China