Mai kanti Baru, shi ne shugaban rukunin kamfanonin albarkatun mai na Najeriyar (NNPC), ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar, jim kadan bayan wata ganawa da ya yi da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari inda ya bayyana masa halin da ake ciki game da fannin albarkatun man kasar.
Baru ya bayyana wa shugaba Buhari irin kwanciyar hankali da aka samu a bangaren man fetur na kasar musamman a 'yan kwanakin nan.
Jami'in na NNPC ya shedawa shugaban kasar game da halin da ake ciki na rarraba albarkatun mai a duk fadin kasar, da kuma yadda ake aikin hako danyen mai da iskar gas har ma da yadda ake samar da iskar gas ga fannin lantarki na kasar. Ya ce shugaban Najeriya ya yi matukar nuna farin ciki game da samun wannan labari na ci gaban da aka samu a fannin albarkatun mai da iskar gas na kasar. (Ahmad Fagam)