in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu sakamakon kai farmaki kan 'yan Shi'a a Syria ya karu zuwa 112
2017-04-17 10:47:41 cri
A ranar 15 ga wata, ayarin motoci masu daukar 'yan Shi'a sama da dubu daya ya gamu da fashewar bom da aka dasa a mota a yankin Rashideen dake yammacin Aleppo na kasar Syria. A ranar 16 ga wata, wani jami'in kasar ya ce, yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon lamarin ya karu zuwa 112, yayin da wasu sama da 100 suka ji rauni.

Bisa wani labari na daban da kamfanin dillancin labarai na Syria ya bayar an ce, jami'ai da fararen hula na birnin Allepo dake arewacin kasar Syria, sun yi gangami a wannan rana, domin la'antar farmakin da aka kai ga 'yan Shi'ar.

A nasa bangaren, babban sakataren MDD Antonia Guterres ya bayar da sanarwa ta bakin kakakinsa a ranar 15 ga wata, inda ya zargi lamarin, tare kuma da yin kira da a yanke hukunci kan wadanda suka kaddamar da harin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China