in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya gabatar da sunan sabon shugaban UNDP
2017-04-19 13:19:33 cri
A jiya Talata, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya gabatar da sunan sabon shugaban UNDP, hukumar shirin raya kasa ta MDD wato 'dan kasar Jamus Achim Steiner, kuma ana bukatar da tabbatar da kudurin a gun babban taron MDD.

Kakakin babban sakataren MDD Stéphane Dujarric, ya bayar da sanarwa a gun taron manema labarun da aka gudanar a wannan rana, inda ya bayyana cewa, bayan da Guterres ya yi shawarwari tare da kwamitin gudanarwa na hukumar shirin raya kasa ta MDD, ya riga ya mika wasika ga shugaban babban taron MDD, kuma ya bukaci babban taron MDD da ya zartas da kudurin.

Idan aka zartas da kudurin, Steiner zai maye gurbin Helen Clark da zama sabon shugaban hukumar shirin raya kasa ta MDD, da wa'adinsa ya kai shekaru 4. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China