in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karin wurare 8 sun shiga jerin wuraren adana kayan tarihi na ilimin binciken kasa na UNESCO
2017-05-06 12:27:10 cri

Hukumar bunkasa ilimin kimiyya da raya al'adu ta MDD wato UNESCO ta sanar da karin wasu wurare 8 cikin jerin wuraren adana kayan tarihi na ilimin binciken kasa.

Majalisar kula da wuraren kayayyakin binciken kasa na UNESCO ne ya yanke shawarar karin, bayan kammala taronsa na farko a Torquay na Birtaniya a watan Satumban da a gabata, inda kuma kwamitin zartarwa na majalisar ya amince da shi a jiya Jumma'a.

Kasar Sin ta shiga cikin jerin wuraren da yankunanta biyu na Arxan dake jihar Mongolia ta gida, da Keketuohai na jihar Xinjiang ta kabilar Uygur, wadanda yankuna ne masu cin gashin kansu.

Da wannan karin na wurare 8, adadin wuraren ya karu zuwa 127 a kasashe 35.

Hukumar UNECSO ta ce, wuraren adana kayayyakin tarihi na binciken kasa, yankuna ne dake inganta albarkatun karkashin kasa ta hanyar shirye-shiryen al'ummomi da za su inganta ci gaba mai dorewa a yankuna. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China