in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron kasa da kasa karo na 39 na abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni
2015-06-29 13:35:06 cri
A jiya ne, a birnin Bonn dake kasar Jamus, aka kaddamar da taron kasa da kasa karo na 39 na hukumar kula da abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni na kasashen duniya karkashin inuwar UNESCO wato kungiyar kula da ilmi,kimiyya da al'adu ta M.D.D, inda aka yi nazari tare da tantance sabbin ayyukan da suka shafi yanayin da al'adu na kasashen duniya yake ciki, tare da sa ido da ba da shawara game da aikin kare abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni.

Kare abubuwan da aka gada daga kaka da kakani daga barnatarwar kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ya zama wani batun da aka dora muhimmanci sosai a kai. A gun bikin bude taron, babbar direktar kungiyar UNESCO Irina Bokova ta ce, bata abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni wani bangare ne na tashin rikicin da ya shafi jin kai, kuma wannan na da nasaba da aikin kare rayuwar dan Adam.

A gun bikin bude taron, shugaban taron kungiyar UNESCO karo na 37 kuma mataimakin ministan ilmi na Sin Hao Ping ya yi jawabin cewa, bala'u daga indallahi da yadda ake lalata abubuwa sun kawo babban kalubale ga aikin kare abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni, sannan hare-haren ta'addanci da aka kaiwa a kasashen Tunisiya, Faransa, Kuwaitt, sun sake nuna muhimmancin al'adu da sa kaimi ga samar da zaman lafiya da jituwa a duniya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China