Da yake tsokaci yayin wani taron masu ruwa da tsaki game da harkokin sadarwa a jihar Legas dake kudancin Najeriya a jiya Alhamis, farfesa Dambatta ya ce a yanzu haka, Najeriyar na da cibiyoyin turakun sadarwa 50,000 ne, kasa da 80,000 da kasar ke bukata.
Ya ce samar da isassun irin wadannan cibiyoyi, zai baiwa kasar damar shiga jerin kasashe da ke cin cikakkiyar gajiya daga hidimomin sadarwa da ake wa lakabi da (IoT).
Jami'in ya kara da cewa, tsarin samar da hidimomin fasahar sadarwa na IoT, na share fagen cin gajiya daga sadarwar yanar gizo mai karfin 4G da 5G.(Saminu Alhassan)