in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci Najeriya da ta zakulo 'yan wasan kwallon kwando
2017-04-21 09:40:21 cri
An bukaci hukumar wasan kwallon kwando ta Najeriya da ta zakulo 'yan wasa a wani mataki na bunkasa wasan kwallon kwandon a kasar.

Babban sakataren kungiyar wasan kwallon kwando ta Jami'oin kasar(NUGA) Bola Orondele shi ne ya yi wannan kiran jiya Alhamis a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, yana mai cewa wasu daga cikin 'yan wasan da ke wasa a kuloblikan kasar ba su da tsayin da ake bukata a wasan.

Orodele ya kuma shaidawa manema labarai cewa, muddin Najeriya tana bukatar yin fice a gasannin kasa da kasa,yana da muhimmanci ta farauto'yan wasan da suka kware wadanda za su wakilci kasar baya ga kara bunkasa wannan wasa.

Babban sakatare ya ce Najeriya tana bukatar kwararrun 'yan wasa wadanda za su iya fafatawa tare da taka rawar gani a gasannin kasa da kasa, musamman masu tsayi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China