in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya: Cutar Sankarau ta yi sanadin mutuwar mutane 33 a jihar Niger
2017-04-15 12:04:12 cri

Daraktan hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Niger dake arewa maso tsakiyar Nijeriya Yahaya Mu'azu, ya ce mutane 33 ne suka mutu a jihar, biyo bayan barkewar cutar sankarau a wasu sassa na kasar dake yammacin Afrika.

Yahaya Mu'azu, ya ce nau'in cutar da ake wa lakabi da Type C, wanda ya bullo a baya-bayan nan ne ya yi sanadin mutuwar mutane 9, yayin da nau'o'in cutar na type A da B suka yi sanadin mutuwar sauran mutanen 24.

Ya ce jimilar mutane 116 ne aka yi zargin sun kamu da cutar a jihar ta Niger.

Daraktan ya kara da cewa, wasu daga cikin mutanen matafiya ne da suka fito daga jihar Sokoto dake arewa maso yammacin kasar, inda ya kasance daya daga cikin wuraren da barkewar cutar ta fi kamari.

A nasa bangaren, Ministan lafiya na kasar, Isaac Adewole ya ce jimilar mutane 489 ne cutar ta yi sanadin mutuwarsu a fadin kasar.

Ya kuma bayyana cewa, nau'in cutar na Type C sabon ne da ba a saba gani a Nijeriya ba, inda ya ce an shigar da shi ne daga makwabciyar kasar Niger, kuma ya na bukatar nau'in rigakafi na daban. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China