Sakatare a ma'aikatar harkokin fasahar sadarwa a Kenya Joe Mucheru, shi ne ya yi wannan kira, yayin wani taro na tattaunawa game da hanyoyin inganta kayayyakin aiki a makarantun kasar. Mr. Mucheru ya ce akwai bukatar sassa masu zaman kansu su kara yawan jarin da suke zubawa a wannan fanni, domin tallafawa kokarin da gwamnati ke yi.
Jami'in ya ce ya zama wajibi a zuba jari domin samar da kayayyakin da ake bukata, ta yadda za su dace da kalubalen tsaro da ake fuskanta a kasar.
Kaza lika ya bayyana cewa Kenya na da dokar tsaron na'urori masu kwakwalwa da yanar gizo ta shekarar bara, wadda tuni aka turawa majalissar dokokin kasar domin tantancewa, fatan dai shi ne samar da kwararan dokoki na hukunta masu aikata laifuffuka ta intanet.
Kenya na sahun gaba tsakanin kasashen nahiyar Afirka a fagen aikata laifuka ta yanar gizo, sakamakon yadda ake amfani da wannan kafa wajen aiwatar da harkoki da dama, da suka shafi al'amuran rayuwa a kasar. (Saminu Hassan)