Wata sanarwa da ministan ya fitar a jiya Alhamis, ya ce kokarin zai samu nasara ne idan manyan kamfanonin mai na kasashen waje dake aiki a kasar za su gina wasu matsakaitan matatun mai.
Ya ce matatun sun fi kanana girma sai dai, ba za su iya tace adadin mai da matatun Nijeriya ke tacewa ba.
Ya ce ana gina irin su ne domin kara adadin mai da ake tacewa a cikin gida da nufin rage shigar da shi daga ketare.
Ibe Kachikwu wanda ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da jami'an kamfanin mai na ExxonMobil, ya bayyana bukatar da ke akwai na kamfanonin mai na kasashen ketare dake aiki a kasar su fadada zuba jari a bangaren mai da isakar gas.
Ministan ya gana da kamfanin Eni na Italiya a watan Junairun da ya gabata, inda kamfanin ya yi alkawarin aiki da gwamnatin kasar wajen inganta aikin matatar mai ta Fatakwal.
Haka zalika, ya kuma shirya ganawa da kamfanonin Shell da Chevron da kuma Total. (Fa'iza Mustapha)