in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Burtaniya, sun lashi takobin hada hannu wajen yakar sauyin yanayi
2016-12-21 10:08:25 cri
Kasar Sin da Burtaniiya, sun sha alwashin inganta dangantakarsu tare da hada hannu wajen yakar sauyin yanayi.

Wannan ya biyo bayan tattaunawa da memban majalisar gudanarwa ta kasar Sin Yang Jiechi ya yi da firayin ministar Burtaniya Theresa May, bayan kammala wani muhimmin taro karo na takwas da aka yi a birnin London, tsakanin kasar Sin da Burtaniya.

Yang Jiechi, ya ce tabbacin da kasashen biyu ke da shi ya karawa dangantakar su armashi. Inda ya ce a shirye kasar Sin take ta ci gaba da alkinta ziyarar da suke tsakaninsu kan muhimman batutuwa, tare da fadada huldarsu ta fannonin da suka hadar da makamashin nukilya da layin dago, cinikayya da kuma kere-kere.

Ya kuma yi kira ga bangarorin biyu su karfafa tuntubar juna da kyutata tsare-tsare domin magance matsalolin kasashen waje da na yankunansu, da nufin inganta tattalin arzikin duniya tare da yakar kalubalen da duniya ke fuskanta ciki har da sauyin yanayi.

A nata bangaren, firayin minstan Burtaniya Theresa May, ta ce kasarta na sa ran inganta alakarta da kasar Sin kan bangarori da dama, inda ta ce a shirye Burtaniya take, ta hada hannu da sauran kasashe wajen magance kalubalen da suka hadar da sauyin yanayi. (Fa'iza)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China