Dr. Mwamaka Sharifu, wadda a halin yanzu take karatun digirinta na uku a bangaren kiwon lafiyar mata masu juna da cutukan da suka shafi mata a kolejin kiwon lafiya ta Tongji a jami'ar kimiyya da fasaha ta Huazhong ta kasar Sin, ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, magungunan kasar Sin suna da matukar amfani idan aka kwatanta da wasu magungunan da ba irinsu ba.
Sharifu ta fadi hakan ne a lokacin bikin miki tallafi daga gidauniyar Sino-Africa Firefly Charity ga wadanda suka gamu da ibtila'in gobara a Kibera slums.
A lokacin bikin ne kuma aka baiwa Sharifu mukamin jakadar gidauniyar bada tallafin ta Sino-Africa Firefly Charity.
Ta ce zata yi amfani da wannan dama wajen kara karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika.
Sharifu ta ce magungunan kasar Sin sun fi tasiri a kasar ta Kenya a halin yanzu, saboda suna aiki sosai wajen warkar da cututtuka wadanda ba'a daukarsu daga wasu wadanda kuma ake yawan samun karuwarsu.