in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi gargadi game da tabarbarewar al'amurra a Sudan ta kudu
2017-03-18 13:32:39 cri
Babban jami'in tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Sudan ta kudu David Shearer, ya sanar a jiya Juma'a cewa, halin da ake ciki a kasar yana cigaba da tabarbarewa a sakamakon karuwar barkewar tashin hankali da ake samu a shiyyoyin arewacin kasar a cikin yan kwanakin nan.

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya shedawa taron manema labarai cewa, fadan da ya barke a yankunan Equatoria da Upper Nile, yayi sanadiyyar tserewar fararen hula masu yawa da kuma karuwar sabbin kungiyoyin masu dauke da makamai, lamarin da ya sake raba kawunan jama'ar kasar.

Jami'in tawagar MDDn ya yi gargadin cewa, ana amfani da rarrabuwar kawunan kabilun kasar ne domin cimma muradu irin na siyasa.

Kididdigar baya bayan nan ta hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, ta nuna cewa, kimanin mutane miliyan 1.6 ne rikicin Sudan ta kudu ya raba su da matsugunnansu, wadanda a halin yanzu suke warwatse a sassa daban daban dake dake kasar.

A cewar Shearer, duk da irin yanayin tabarbarewar al'amurra a kasar, jami'an MDD dake cigaba da gudanar da ayyukasu a kasar suna fuskantar koma baya na rashin samun damar shiga wasu yankunan kasar don kai kayan agaji, saboda rashin samun cikakken goyon bayan daga mahukuntan Sudan ta kudun

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China