Babban jami'in shirin jin kai na MDD dake kasar ta Sudan ta kudu, Eugene Owusu, ya ce kashe jami'an bada agaji ya faru ne a lokacin rabon muhimman kayayyakin abinci a garin Wau kasa da mako guda bayan kiran da aka yi na kawo karshen kaddamar da hare hare kan jami'an agajin a Sudan ta kudu.
A wata sanarwar da ya fitar a Juba, Owusu ya ce ya yi matukar kaduwa game da wannan mummunan al'amari, don haka ya bukaci a gaggauta binciko wadanda suka aikata wannan danyen aiki domin hukunta su.
An hallaka jami'an uku ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa dakin ajiya na shirin hukumar samar da abinci ta duniya WFP, a lokacin da ake tsaka da fuskantar matsalar tsaro a garin Wau a ranar 10 ga wannan watan
Da wannan mutuwa, kawo yanzu ma'aikatan jin kai da aka hallaka a Sudan ta kudu sun kai 82, kuma a shekarar nan ta 2017 kawai, an hallaka jami'an agaji 14. (Ahmad Fagam)