John Ging, ya ce yayin da Somalia ke tunkarar matsalar a yanzu, Sudan ta kudu ba ta iya wa.
Jami'in ya bayyana haka ne jiya Talata a hedkwatar MDD dake birin New York, lokacin da yake yi wa manema labarai bayani game da rangadin gaggawa da ya kai kasashen.
Ya ce matsalar karancin abinci ta yi kamari a kasashen, ya na mai cewa kimanin mutane miliyan 6.2 ne ke bukatar agajin jin kai a Somalia, kuma saboda rikici da ake fama da shi, an samu barkewar cutar amai da gudawa, inda mutane 25,000 suka kamu da ita. (Fa'iza Mustapha)