in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin farko na dakarun RPF sun isa Sudan ta kudu
2017-04-30 13:03:48 cri
Rahotanni daga kasar Sudan ta kudu na cewa, a jiya ne rukunin farko na dakarun tsaro (RPF) na tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke Sudan ta kudu(UNMISS) suka fara isa kasar.

Tawagar ta UNMISS wadda ta bayyana hakan, ta ce tun a ranar 20 ga watan Afrilu ne rukunin share fage na kamfanin gine-gine daga kasar Bangladesh ya fara isa kasar, inda ya kai muhimman kayayyaki don fara aikin gina gidajen kwana da wurare da dakarun za su yi aiki a birnin Juba.

Tawagar ta ce ana saran a watan Yuni da Yuli dakaru daga kasar Rwanda su ma za su isa kasar, kuma tuni aka kafa hedkwatar rundunar ta RPF a birnin Juba,babban birnin kasar Sudan ta kudu karkashin jagoranci Janar Jean Mupenzi dan kasar Rwanda.

A watan Agustan shekarar 2016 ne kwamitin sulhu na MDD ya amince da tura dakaru 4,000 na RPF bisa bukatar da kungiyar IGAD ta gabatar masa, domin farfado da birnin Juba bayan sabon fadan da ya barke a can.

Bayanai na nuna cewa, tura Karin dakarun zai kara karfin dakarun tawagar UNMISS mai dakaru 13,000 dake aiki a kasar da yaki ya wargaza.

Tawagar ta UNMISS ta bayyana cewa, kasashe kamar Nepal da Pakistan sun bayyana aniyarsu ta samar da wasu kwararrun da ake karancinsu a shiyyar.

A ranar 30 ga watan Nuwamban shekarar 2016 ne gwamnatin wucin gadi na Sudan ta kudu ta tabbatarwa kwamitin sulhun MDD cikin wata sanarwa cewa, ta yarda da shirin kwamitin na tura dakarun ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Aikin dakarun na RPF dai shi ne kare muhimman gine-gine dake birnin Juba da kuma kula da hanyoyin shiga da fita na birnin. Sauran sun hada da karfafa matakan tsaron da MDD ke yi na kare rayuka da matsugunan fararen hula da sauran harabobin MDD.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China