Wata sanarwar da ofishin bankin dake Ghana ya fitar jiya Alhamis, ta ce wasu al'ummu da aka zaba a yankunan karkara na Brong-Ahafo da yankin yammacin kasar ne za su ci gajiyar tallafin na dala miliyan 5.5.
An tsara shirin ne, ta yadda zai karfafa ilimi da harkokin al'ummun wajen rage lalacewar dazuka da inganta kula da harkokinsu.
Haka zalika, shirin na da nufin kara musu kwarin gwiwa wajen tunkarar matsalolin da dan Adam da kuma sauyin yanayi ke haifarwa
Daraktan Bankin a kasar Ghana Henry Kerali, ya ce shirin zai bada gudunmuwa ga shirin kawance na bankin a kasar Ghana, tare da magance batutuwan sauyin yanayi ta hanyar tallafawa shirye-shirye masu jibi da samar da ruwa da da kare lallacewar filaye. (Fa'iza Mustapha)