Sanarwar wanda ministan kudin kasar Kenneth Ofori-Atta ya sanyawa hannu ta ce, nan da wasu 'yan makonni ne gwamnatin Ghanan zata nada sabon gwamnan babban bankin kasar.
Sanarwar ta yiwa gwamnan babban bankin kasar mai barin gado Abdul-Nashiru Issahaku fatan alheri, wanda a halin yanzu ya gabatar da takardar barin aiki, kana sanarwar ta tabbatarwa masu ruwa da tsaki a harkokin kudin Ghanan cewa, sabon gwamnan da za a nada, zai dora ne kan nasarorin da Issahaku ya cimma, wajen sadaukar da kai da yin aiki tukuru domin daidaita yanayin bunkasuwar tattalin arzikin kasar
Sanarwar ta kara da cewa an gudanar da sauye sauye masu yawa wadanda suka inganta sha'anin kudi da tattalin arzikin kasar a lokacin da yake jagorantar babban bankin kasar.