in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Duniya zai kara tallafin da ya ke bai wa kasar Ghana
2017-04-04 12:51:41 cri

Daraktan Bankin Duniya a kasar Ghana Henry Kerali, ya ce zuwa badi, bankin duniya zai fadada tallafin raya kasa da ya ke ba kasar Ghana da kashi 40 cikin dari.

Da yake jawabi a wani bangare na taron nazarin mizanin nasarar tattalin arzikin kasar Ghana a jiya Litinin, Henry Kerali ya ce, zuwa badi, bankin duniya zai kara tallafin da hukumarsa ta raya kasashe IDA ke ba kasar da kashi 40 a kan jimilar dala biliyan 1.2 da za a kashe cikin shekaru uku.

A don haka, ya ce suna sa ran tattalin arzikin kasar zai ci gaba da habaka yayin da tallafin bankin zai karu.

Mataimakin ministan kudi na kasar Charles Adu Boahen, ya bukaci a yi amfani da tallafin yadda ya kamata, ta yadda za a samu sakamako mai kyau.

Ya ce yana son tunatar da cewa, kudaden tallafi ko na rance kudade ne na al'umma, a don haka ya kamata a yi amfani da su bisa sabuwar dokar kashe kudin al'umma da kuma ka'idojin da masu bada tallafin suka gindaya.

A nasa bangaren, babban jami'in kula da harkokin bankin duniya a Ghana, ya ce cikin shekaru hudu da suka gabata, kasar Ghana ta samu gagarumar nasara wajen aiwatar da shirye-shiryen raya kasa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China