Ministar ta bayyana hakan ne yayin da ta ke jawabi a taron karawa juna sani game da adana bayanai na kasa da kasa karo biyu wanda hukumar kare bayanai ta shirya. Ta kuma lura da cewa, muhimman bayanai tamkar makamashi ne da ke bunkasa harkokin kasuwanci ta yanar gizo a wannan zamani, don haka ta nuna damuwa kan yadda ake da bukatar kara tsaron bayanai.
Ministar ta kuma yi kiran da a kara daukar matakan kare bayanai, ganin yadda harkokin kasuwanci na kasa da kasa suka dunkule a waje guda. A cewarta yana da muhimmanci a kara fahimtar yadda kasashe da shiyoyi da kasa da kasa ke kokarin bullo da matakai da dokoki wadanda za su saukaka harkokin kasuwanci da cinikayya.(Ibrahim)