in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafafen watsa labarun Argentina sun jinjinawa Messi
2017-04-27 10:46:41 cri
Wasan El Clasico da Barcelona ta doke Real Madrid a karshen mako ya ja hankalin duniya, inda a Argentina kasar gwarzon Barcelona Leonel Messi, jaridu da mujallun kasar, suka buga bayanai daban daban, suna jinjina masa.

Messi dai shi ne ya zame wa Barcelona tauraro a wasan na ranar Lahadi, domin kuwa shi ne ya ciwa kungiyar ta sa kwallo ta 3, bayan ta biyu da ya zurawa Real Madrid din, a wasan da Barca ta lashe da ci 3 da 2.

Jaridar Ole ta Argentinas ta ce "Wasan ya tattara komai: damuwa, ja-in-ja, jan kati, da kuma, kwarewa da Lionel Messi ya nuna," Ole ta ce Messi wanda ke rike da lambar yabo ta Ballon d'Or har karo 5, ya sake nuna banbancin sa daga saura a wasan na hamayya.

Ita ma jaridar Clarin jinjinawa dan wasan mai shekaru 29 da haihuwa ta yi, tana mai cewa "Ya sake nunawa duniya" ya dara Cristiano Ronaldo, ganin yadda yawan kwallayen sa suka kai 500, a yayin wasan na karshen mako.

Clarin ta kara da cewa, "Birnin da ya fito da Cristiano Ronaldo, yanzu ma ya sake rusunawa a gaban Messi, domin nuna girmamawa ga babban sadauki,".

Shi kuwa Juan Pablo Varsky cewa ta yi, Messi ya misa sakon musamman yayin da yake murnar nasarar sa, lokacin da ya cire regar dake jikin sa yana daga wa 'yan Real Madrid. "Ya yi murna ta hanyar kalubalantar kowa," "Sadauki ne a irin nasa ajin. Ya kuma kammala wannan wasa da nasarar da ta cancanta. Lallai tauraruwar sa na dada haskawa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China