Da yake zantawa da gidan talabijin na Esporte Interativo a karshen makon jiya, Neymar ya ce batun komawar sa Barcelona na da matukar sarkakiya, kuma mutane da yawa ba za su iya fahimtar wasu batutuwan dake da nasaba da hakan ba. A hannu guda kuma ya ce ba lallai ne kawai don wasu na ganin dacewar ya taya kulaf din Santos murya yayi hakan ba.
Neymar, da mahaifin sa Neymar Santos, da kungiyar Barcelona sun shiga takun saka da ta kai ga zuwa gaban kuliya, bisa rashin fahimta da ta shiga tsakanin su da kungiyar Santos, kungiyar da ta ce tana bin dan wasan tsabar kudade masu tarin yawa, sakamakon cinikin komawar sa Camp Nou a shekara ta 2013.
Baya ga kungiyar Santos, shi ma kamfanin DIS investment na Brazil din ya yi korafin cewa an ci da gumin sa, yayin cinikayyar dan wasan mai shekaru 25 da haihuwa. An dai bayyana cewa an yi cinikin Neymar kan kudi har Euro miliyan 57, kafin wasu bayani su nuna cewa kudin sun kai Euro miliyan 83.(Saminu Alhassan)