A wasan da kungoyoyin suka buga dai ranar Litinin 24 ga watan nan, an tashi ne kunne doki masar ci a wasan na ranar Asabar. Cikin 'yan wasan da ba su taka leda a wasan ba harda kyafitin din Persepolis Seyyed Jalal Hosseini, da dan wasan gaban ta Soroush Rafiei, wadanda aka dakatar bayan samun katin gargadi bi-biyu yayin wasan kungiyar da ya gabata, a filin wasa na Al Rayyan dake birnin Tehran.
An dai buga wasan rana ta 5 a Litinin din ne a filin wasa na Qaboos dake Muscat, a kasar Oman. Kafin hakan Persepolis ta tashi kunnen doki 1 da 1 da Al Hilal, a wasan farko da suka buga.
Bisa wasannin da aka riga aka buga yanzu haka, a rukunin A kungiyar Al Ahli ta Dubai ce ke kan gaba da maki 7. A rukinin B kuwa Lekhwiya SC ta Qatar ce a sama da maki 8. Sai Al Ain ta hadaddiyar daular Larabawa dake saman rukunin C da maki 9.
A rukunin D kuwa kungiyar Al Hilal ta saudiyya ce ke kan gaba da maki 9. Sauran kungiyoyin dake sama a teburin rukunonin sun hada da Muang thong United ta Thailand dake saman rukunin E da maki 8. Yayin da kuma Urawa Red Diamonds ta Japan ke jagorantar rukunin F da maki 9. Sai kuma Suwon ta kasar Koriya ta kudu dake kan gaba a rukuni na G da maki 8. Kungiyar Jiangsu FC ta Sin kuma ita ce mafi yawan maki a yanzu haka, inda take saman teburin rukunin H da maki 12. (Saminu Alhassan)