An dai baiwa dan wasan dan asalin kasar Brazil katunan kargadin ne a wasan cin kofin La liga na kasar Sifaniya, wanda Barcelona ta sha kasha hannun Malaga da ci 2 ba ko daya a karshen mako. Hakan kuma na nufin ba zai halarci wasan da Barcelonan za ta je gidan Malaga ba, wanda za a buga a ranar 23 ga watan nan.
Baya ga haka Neymar zai rasa damar buga wasan da Barcelona za ta buga a ranar Asabar da Real Sociedad, da wanda kungiyar sa za ta buga da Osasuna a ranar 26 ga watan nan na Afirilu.
Ana dai ganin mai yiwuwa ne Barcelona ta kalubalanci wannan hukunci, amma ko da hakan ta faru, mai yiwuwa Neymar ya gaza samun damar bugawa kungiyar ta sa ragowar wasanni, wadanda za su ba ta damar kaiwa ga nasarar daukar kofin na La Liga.
Yanzu haka dai Real Madrid ce a saman teburin na La liga da maki 72, sai Barcelona a matsayi na 2 da maki 69, yayin da Atletico Madrid ke matsayi na 3 da maki 62.(Saminu Alhassan)