in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uganda KCCA ta doke Al Masry ta Masar a gasar zakarun Afirka
2017-04-13 09:11:29 cri

Kungiyar kwallon kafa ta KCCA FC ta samu nasara kan takwarar ta ta Al Masry SC dake Masar, da ci 1 da nema, a zagayen farko na gasar zakarun kulaflikan nahiyar Afirka wanda hukumar CAF ke shiryawa.

Dan wasan Uganda KCCA Derrick Nsibambi ne ya zura kwallo daya tilo da aka ci a wasan, a ragar Masry SC, mintuna 4 cikin Karin lokaci da aka yi a karshen wasan.

Haka kuma aka tashi wasan da aka buga a filin wasa na Philip Omondi dake Uganda da ci daya da nema, ranar Asabar din karshen mako.

Dan wasan gaban Uganda Geoffrey Sserunkuma ya samu dama har sau biyu ta zura kwallo a zare amma hakan ta gagara, yayin da su ma Brian Majwega da Paul Masiko, suka doka wasu kwallaye da suka fice waje, yayin da ake ganin kwallayen a matsayin wadanda suka dace su daga ragar kungiyar Masry SC.

A bangaren Masry SC kuwa, Elsayed Abdelaal da Ahmed Abdalraof ne kadai, suka yi kokarin kai wasu hare hare masu zafi.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Masry SC ta matsa kaimi matuka, sai dai kuma ta gaza karya lagon bayan KCCA FC, lamarin da ya kai ga sai da a mintuna 4 cikin Karin lokacin wasan KCCA FC ta samu damar jefa kwallo da ta raba gardamar wasan.

Bayan kammalar wasan, kocin Masry SC Hossam Hussien Hassan, ya shaidawa kamfanin dillancin rabarai na kasar Sin Xinhua cewa, 'yan wasan sa sun yi rashin sa'a a Kampala, yana mai danganta hakan da yanayin filin wasan birnin Kampalan, wanda ya sanya yan wasan sa da dama jin rauni. Sai dai ya ce za su dauki fansa a gida. KCCA FC wadda a gasar Total wadda hukumar CAF ke shiryawa ta sha kashi hannun Mamelodi Sundowns ta Afirka ta kudu tun a zagayen farko na gasar, yanzu haka na ta kokarin ganin ta samu nasarar fitowa daga rukunin ta a wannan karo.

Yanzu haka dai kunnen doki a gidan Masar zai baiwa kungiyar ta Uganda damar fitowa daga rukunin. Kuma kungiyoyin biyu za su sake karawa ne a karo na biyu a wasan Asabar din karshen makon nan a Masar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China