in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Argentina ta sallami koci Bauza
2017-04-13 09:09:47 cri
Hukumar kwallon kafar kasar Argentina ta AFA, ta sallami mai horas da 'yan wasan tawagar kasar Edgardo Bauza daga mukamin sa, sakamakon yadda ya gaza samun nasarorin da ake bukata.

An bayyana daukar wannan mataki ne kasa da makwanni 2, bayan da Argentina ta kwashi rashin nasara a wasan ta da Bolivia, wanda suka buga a filin wasa na La Paz, wasan da aka tashi Bolivia na da kwallo 2 Argentina na nema, lamarin da ya jefa kungiyar ta Argentina cikin hadarin rashin samun gurbin buga gasar cin kofin duniya dake tafe cikin shekara mai zuwa.

Tuni dai shugaban hukumar ta AFA Claudio Tapia ya shaidawa manema labarai daukar wannan mataki, ya kuma alkawarta kiran taron manema labarai domin fayyace batun dalla dalla.

Cikin wadanda ake hasashen za su iya maye gurbin Bauza, akwai kocin kungiyar Sevilla Jorge Sampaoli, da kuma na Atletico Madrid Diego Simeone.

Bauza, wanda ya maye gurbin Gerardo Martino a watan Agustan bara, ya jagoranci Argentina wasanni 3 da suka ci nasara, da kunnen doki 2, da kuma rashin nasara 3.

Bayan rashin nasara a wasan su da Bolivia, Argentina da ta dauki kofin duniya har karo 2, ta yi kasa zuwa matsayi na 10, a jerin kungiyoyin kudancin latin Amurka, kuma a yanzu haka tana da ragowar wasannin share fagen shiga gasar cin kofin duniya wanda hukumar FIFA ke shiryawa guda 4.

A wannan gaba kuma kungiyar na fuskantar karin matsi, bayan da aka dakatar da babban dan wasan ta Lionel Messi har wasanni 4, sakamakon rashin da'a da ya yiwa alkalin wasa cikin wasannin kungiyar na baya. Koda yake dai hukumar ta AFA ta ce za ta kalubalanci wannan dakatarwa.

Kungiyoyi 4 mafiya samun maki ne dai za su wakilci yankin na kudancin latin Amurka, tare da samun gurbin buga gasar ta badi wadda kasar Rasha za ta karbi bakunci. Kana ta 5 za ta buga karin wasa da takwararta ta yankin Oceania, kafin samun gurbin shiga gasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China