Yan sanda sun ce motar tawagar yan wasan ta Dortmund in shirya kai mata hari ne, inda wani dan wasan mai shekaru 26 da haihuwa ya dan wasan Spaniya na kasa da kasa Marc Bartra ya samu rauni.
Mai magana da yawun kungiyar wasan kwallon kafan kulob din Sascha Fligge yace an yiwa Bartra tiyata a wuyan hannunsa, kuma dukkannin yan wasan sun yi matukar firgita.
Da misalin karfe 7 na yamma a gogon wajen a gundumar Hoechsten dake Dortmund, jim kadan bayan da tawagar yan wasan ta tashi zuwa Borussia Dortmund daga otel din da suke zaune yayin da suka nufi filin wasan Signal Iduna Park don buga wasan na UEFA Champions League na kusa dana karshe inda zasu kara da AS Monaco na kasar Faransa, abubuwan fashewar uku sun lalata windon motar yan wasan.
Sai dai har yanzu babu wasu alamu dake nuna ko harin yana da nasaba da da harin ta'addanci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Jamus (DPA),ya rawaito.
Yan sanda sun bada rahoto ta shafukan sada zumunta na zamani cewa, an yi mafani da munannan ababan fashewa wajen kai harin, wanda aka ajiye a kusa da inda ake ajiye ababan hawa.
Yanzu dai an dage wasan da za'a buga zuwa ranar laraba kuma dukkanin wasannin da za'abuga a wannan rana an dagesu.(Ahmad Fagam)