Bankin ya ce rahoton bincike na ma'aunin nazarin harkokin kamfanoni (PMI) ya nuna cewa za a samu ci gaba na bai daya. Rahoton na sa ran cewa a cikin shekarar 2017, alkaluman GDP na kasar Sin za su kai kashi 6.6 cikin dari.
Ya kara da cewa, ci gaban ma'aunin sauyin farashin kayayyaki da bada hidima (CPI), ka iya farfadowa ya kai kashi 1.3 cikin dari a watan Maris, daga kashi 0.8 cikin dari da yake ciki a watan Fabreru, a daidai lokacin da aka samu bacewar matsalolin da aka samu lokacin bikin sabuwar shekara na kasar Sin.
A cikin watanni uku na karshen shekarar 2016, tattalin arzikin kasar Sin ya kai kashi 6.8 cikin dari. Inda a bana, gwamnatin kasar ta sa ran samun karin kashi 6.5 cikin dari. ( Fa'iza Mustapha)