Taron majalisar gudanarwar kasar da ya gudana a jiya Laraba karkashin jagorancin Firayiministan kasar Li Keqiang, ya samar da wasu tsare-tsare da za su tabbatar da sauyi ga tattalin arzikin kasar a bana, inda ya kuma bayyana sauran fannonin dake bukatar sauyin.
Li Keqiang, ya ce bunkasar tattalin arzikin kasar da sakamakon da ake hasashen samu a bana, sun dogara ne a kan tsare-tsaren da za a aiwatar.
Ya yi nuni da cewa, sauye-sauyen za su tabo dukkan bangarori da za a yi amfani da su, yana mai kira ga dukkan sassan gwamnati su marawa shirin baya.
Bangarori da dama ne yunkurin na inganta tattalin arziki zai taba a bana. (Fa'iza Mustapha)